Publicidade

Honestidade

Por Bíblia Online

A honestidade é virtude cristã fundamental. Deus é Deus de verdade e nos chama a viver com integridade, transparência e retidão em todos os nossos relacionamentos e negócios.

Integridade diante de Deus

O Senhor abomina a balança falsa, mas o peso justo é seu prazer. A integridade dos justos os guia pelos caminhos retos.

Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,

amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.

Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,

amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.

Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,

amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.

Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci

da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.

Yin abin da yake daidai da kuma nagari

Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

Bari idanunka su dubi gaba sosai,

ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.

Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.

Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.

Praticar a honestidade

Falai a verdade, pagai o que deveis, não negueis ao próximo o bem. A honestidade prática é testemunho do evangelho.

Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa

Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.

Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.

Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace,

sa’ad da kana iya yin haka.

Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci

da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.

Dukiyar da aka samu a hanyar da ba dace ba, ba ta da albarka,

amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.

Confissão e transparência

Confessai as vossas ofensas uns aos outros. Quem confessa e deixa o pecado encontra misericórdia e restauração.

Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari "I" naku zama "I". "A’a" naku kuma zama "A’a", don kada a hukunta ku.

Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.

In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.

Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

Coração puro

Bem-aventurados os puros de coração, porque verão a Deus. A honestidade começa no interior e se manifesta nas ações.

Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,

gama za su ga Allah.

Ka natsu a gaban Ubangiji

ka kuma jira da haƙuri gare shi;

kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,

shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.

Fitila a kan wurin ajiye fitila

"Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.

Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi,

amma adali kan kuɓuta daga wahala.

Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,

amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.

Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali,

mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-