Pular para o conteúdo
Publicidade

Honrar os pais

Por Bíblia Online

Honrar pai e mãe é mandamento de Deus com promessa de vida longa e feliz. A Bíblia ensina que respeitar, obedecer e cuidar dos pais é dever sagrado dos filhos.

O mandamento com promessa

Honra a teu pai e a tua mãe para que vá bem contigo e vivas muito tempo sobre a terra. É o primeiro mandamento com promessa.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

Obedecer e respeitar

Filhos, obedecei a vossos pais no Senhor. Ouvir a instrução do pai e não desprezar o ensino da mãe traz sabedoria.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Za su zama kayan ado don su inganta ka

da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

Hikima ce mafi girma duka

Ku saurara ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

ku mai da hankali, ku sami fahimi.

Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,

amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.

Faɗi 17

Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,

kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

Yesu ya amsa ya ce, "Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? Gama Allah ya ce, Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.

Yesu ya amsa ya ce, "Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? Gama Allah ya ce, Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi. Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, Duk taimakon da ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah, ba zai girmama mahaifinsada shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.

Consequências da desonra

A Bíblia adverte severamente contra a desonra aos pais. Quem amaldiçoa ou agride os pais enfrenta consequências sérias.

Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa

ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.

In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,

fitilarsa za mutu a tsakiyar duhu.

"Idon da yake yi wa mahaifi ba’a,

wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya,

hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido,

ungulai za su cinye su.

"Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

Rashin sanin Allah a kwanakin ƙarshe

Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,

Cuidar dos pais

Quem não cuida dos seus, principalmente de sua família, negou a fé. Honrar os pais inclui respeitar os idosos.

Amma in gwauruwa tana da ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

" Dole kowannenku girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.

" Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.

Seja o primeiro