Humildade
A humildade é o caminho da honra verdadeira. Deus resiste aos soberbos, mas dá graça aos humildes. Jesus lavou os pés dos discípulos e nos ensinou que o maior é aquele que serve.
Humilhar-se diante de Deus
Humilhai-vos diante do Senhor e Ele vos exaltará. Quem se humilha será exaltado, e quem se exalta será humilhado.
Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.
Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.
in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
Ubangiji nagari da mai adalci ne;
saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.
Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai
ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci
amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
Humildade como virtude
Considerai os outros como superiores a vós mesmos. Revesti-vos de humildade, mansidão e paciência no trato uns com os outros.
Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.
Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.
Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.
Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.
Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
Shan wahala saboda yin ayyuka alheri
A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.
Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
O exemplo de Jesus
Aprendei de mim, que sou manso e humilde de coração. O maior entre vós seja o que serve — esse é o caminho do Reino.
Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne."
"Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.
Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, "In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa."
Sai ya ce musu, "Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma."
Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,
amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
Humildade verdadeira
O que se exige de ti? Praticar a justiça, amar a misericórdia e andar humildemente com teu Deus.
Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
Umarnai don iyalan masu bi
Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.
Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.
Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.
Hikima iri biyu
Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.