Incentivo
A Bíblia é fonte inesgotável de incentivo. Em cada página, Deus nos encoraja a não temer, a perseverar e a confiar que Ele está conosco e é maior que qualquer adversidade.
Deus é por nós
Se Deus é por nós, quem será contra nós? O Senhor fortalece, sustenta e guia seus filhos em cada batalha e desafio.
Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."
Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
Esperança e perseverança
A tribulação produz perseverança, a perseverança produz caráter, e o caráter produz esperança que não decepciona.
Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
Yesu ya ce, " ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata."
Deus cuida de nós
Entrega o teu caminho ao Senhor. Lança sobre Ele as tuas ansiedades, porque Ele tem cuidado de nós diariamente.
Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;
ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,
zai sa sawu su kahu;
ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba,
gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,
ya kuwa amsa mini.
Ba zan ji tsoro ko dubu goma
suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
Futuro e promessas
Eu sei os planos que tenho para vocês — planos de paz e não de mal, para dar-lhes futuro e esperança.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa."
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."
Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,
"Ba idon da ya taɓa gani,
ba kunnen da ya taɓa ji,
ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin
abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa."
Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.