Jesus me ama
Jesus me ama — essa certeza transforma vidas. O amor de Cristo não depende do nosso merecimento, mas da sua natureza. Ele nos amou primeiro, e nada pode nos separar desse amor.
Ele me amou primeiro
Nós amamos porque Ele nos amou primeiro. O amor de Deus se manifestou em nos enviar seu Filho como propiciação pelos nossos pecados.
Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.
Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu.
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.
Amor inseparável
Nem a morte, nem a vida, nem qualquer outra criatura poderá nos separar do amor de Deus em Cristo Jesus nosso Senhor.
Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? Kamar yadda yake a rubuce cewa,
"Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka."
A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.
da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya.
Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.
Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
Celebrar o amor de Jesus
O amor de Jesus é motivo de cântico e louvor. De manhã cantarei teu amor e à noite proclamarei tua misericórdia.
Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata,
Allah mai ƙaunata.
Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,
mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
Ba zai yi ta zargi ba
ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu
ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,
haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
kamar yadda gabas yake daga yamma,
haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.