Jesus Cristo
Jesus Cristo é o centro de toda a Escritura — Deus encarnado, Salvador do mundo, Senhor dos senhores. Nele habita corporalmente toda a plenitude da divindade.
A divindade de Cristo
No princípio era o Verbo, e o Verbo estava com Deus, e o Verbo era Deus. Jesus é Deus revelado em carne humana.
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. Yana nan tare da Allah tun farar farawa. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,
Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata, an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,
bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
amma ya mai da kansa ba kome ba,
yana ɗaukan ainihin surar bawa,
aka yi shi cikin siffar mutum.
A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
Jesus, o Filho de Deus
Tu és o Cristo, o Filho do Deus vivo! Jesus revelou o Pai e demonstrou sua autoridade divina por palavras e obras.
Ya tambaye su, "Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?"
Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai."
Yesu ya amsa ya ce, "Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.
"Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel" (wanda yake nufin "Allah tare da mu").
Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, "Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!"
Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.
Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, "Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?"
Yesu ya ce, "Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama."
Ya ce, "Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.
Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, "Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai."
Eu Sou
Jesus disse: antes que Abraão existisse, Eu Sou. Ele se identificou com o nome divino revelado a Moisés na sarça ardente.
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!"
Musa ya ce wa Allah, "A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?"
Allah ya ce wa Musa, "NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ "
Da ni da Uba ɗaya ne."
Yesu ya ce musu, "Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki." Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.
O Salvador e Senhor
Jesus é o caminho, a verdade e a vida. Não há outro nome dado entre os homens pelo qual devamos ser salvos.
Yesu ya amsa ya ce, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.
Yesu ya amsa ya ce, "Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.
Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;
Sai Yesu ya ce, "Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?"
Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto."
Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, "Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?" Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
A supremacia de Cristo
Ele é o resplendor da glória de Deus e a expressão exata do seu ser. Toda a plenitude habita nele e por Ele tudo subsiste.
Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.
Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.
Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.
Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.
Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
Gama a gare mu an haifa mana yaro,
a gare mu an ba da ɗa,
gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.
Za a ce da shi
Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki
Uban Madawwami, Sarkin Salama.
Confessar a Cristo
Todo aquele que confessa que Jesus é o Filho de Deus, Deus permanece nele e ele em Deus. A fé em Cristo é a vitória.
Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.
Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa.
Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.
Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.
Cewa in ka furta da bakinka, "Yesu Ubangiji ne," ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.
Viver em Cristo
Já não sou eu quem vive, mas Cristo vive em mim. Ele supre toda necessidade, dá paz e reina como Senhor.
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.
Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,
O Rei eterno
O Rei dos reis voltará em glória e majestade. Todo joelho se dobrará e toda língua confessará que Jesus Cristo é o Senhor.
Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. "Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe." Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce,
Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
Sa’an nan ya ce wa Toma, "Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata."
Toma ya ce masa, "Ya Ubangijina da Allahna!"
Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ "
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. Da ni da Uba ɗaya ne."
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.
duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su."
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah."
Yesu ya amsa ya ce, "Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah."
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.