Pular para o conteúdo
Publicidade

O juízo final

Por Bíblia Online

O juízo final é a conclusão da história humana. Todos os seres humanos comparecerão diante do trono de Deus para o julgamento eterno — os salvos para a vida, os ímpios para a condenação.

O grande trono branco

Vi um grande trono branco e os mortos diante de Deus. Os livros foram abertos e cada um foi julgado segundo as suas obras.

An shari’anta matattu

Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.

Maganar ƙarshe. Gayyata da gargaɗi

"Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.

Maganar ƙarshe. Gayyata da gargaɗi

"Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.

"Ina cikin dubawa,

"sai aka ajiye kursiyoyi,

sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.

Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;

gashin kansa sun yi fari kamar ulu.

Kursiyinsa kuma harshen wuta,

dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.

"Ina cikin dubawa,

"sai aka ajiye kursiyoyi,

sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.

Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;

gashin kansa sun yi fari kamar ulu.

Kursiyinsa kuma harshen wuta,

dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.

Kogin wuta yana gudu,

yana fitowa daga gabansa.

Dubun dubbai sun yi masa hidima;

dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa.

Aka zauna don shari’a,

aka kuma buɗe littattafai.

Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Preparação para o juízo

Deus estabeleceu um dia para julgar o mundo com justiça. Arrependei-vos, porque o juízo se aproxima e cada palavra será pesada.

Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin da shi daga matattu."

Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka."

Tumaki da awaki

"Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.

Tumaki da awaki

"Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.

"Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.

"Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?

"Sarkin zai amsa ya ce, Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.

"Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.

"Su ma za su amsa, su ce, Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?

"Zai amsa, ce, Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.

"Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami."

Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,

har da waɗanda aka yi a ɓoye,

ko nagari ne, ko mugu.

Sai na yi tunani a zuciyata,

"Allah zai shari’anta

masu adalci da masu mugunta,

gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki,

lokaci domin kowane abu."

"Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

Segurança em Cristo

Quem crê no Filho tem a vida eterna e não entra em juízo. O amor de Deus é nosso refúgio diante do juízo vindouro.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada hallaka sai dai sami rai madawwami.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada hallaka sai dai sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne.

Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ad da ya zo kuwa, zai da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.

Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.

Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.

Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don ɗauki zunubi ba, sai dai don kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

Gama,

"A cikin ɗan lokaci kaɗan,

mai zuwan nan zai zo

ba kuwa zai yi jinkiri ba.

Amma,

"Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.

In kuwa ya ja da baya,

ba zan ji daɗinsa ba."

Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.

Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,

yana zuwa don hukunta duniya.

Zai hukunta duniya cikin adalci

mutane kuma cikin amincinsa.

Seja o primeiro

Este artigo te tocou? Faça uma oração!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.