Juízo
O juízo de Deus é manifestação de sua justiça e soberania. Ele julga o mundo, julga as nações e julga cada coração com perfeita equidade e misericórdia.
O juízo de Deus
Deus é juiz justo que prova os corações. Seu juízo é verdadeiro e alcança toda obra, secreta ou pública.
Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,
har da waɗanda aka yi a ɓoye,
ko nagari ne, ko mugu.
Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
"Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
"Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
"In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;
Yesu ya ce, "An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan. Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni."
Sai mutumin ya ce, "Ubangiji, na gaskata," ya kuma yi masa sujada.
Yesu ya ce, "Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance."
Prestando contas
Cada um prestará contas de si mesmo a Deus. O juízo começa pela casa de Deus e depois alcança os que não obedecem ao evangelho.
Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba. A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.
Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah?
Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.
Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
"Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?
Justiça e redenção
O juízo de Deus é também redenção. Ele livrou Israel do Egito com juízos e salva os arrependidos pela cruz de Cristo.
"Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.
"A wannan dare, zan ratsa Masar, in bugi kowane ɗan fari, na mutum da na dabba, zan kuma hukunta dukan gumakan Masar. Ni ne Ubangiji.
Kai kaɗai na yi wa zunubi
na yi abin da yake mugu a idonka,
ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana
aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki
kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna
saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
Sun ragargaje dukan sassaƙar katako
da gatura da kuma gudumarsu.
Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus;
suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.
Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa,
"Halleluya!
Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,
gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma.
Ya hukunta babbar karuwan nan
wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta.
Ya rama jinin bayinsa a kanta."
Suka sāke tā da murya suka ce,
"Halleluya!
Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin."