Publicidade

Julgamento

Por Bíblia Online

O julgamento pertence a Deus. A Bíblia adverte contra o juízo precipitado entre irmãos e revela que Cristo é o juiz justo que julgará vivos e mortos com perfeita equidade.

Não julgueis

Jesus disse: não julgueis para que não sejais julgados. Com o juízo com que julgais, sereis julgados.

Ɗora wa waɗansu laifi

"Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma.

Ɗora wa waɗansu laifi

"Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.

Ɗora wa waɗansu laifi

"Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.

"Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.

"Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido?

Ba wa waɗansu laifi

"Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

Ba wa waɗansu laifi

"Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

Ba wa waɗansu laifi

"Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."

Julgar com justiça

Quando precisar avaliar, julgue segundo a justa aparência. Não julgue pela carne, mas pelo Espírito e pela verdade.

Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci."

Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a. Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.

Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin ceci duniya ta wurinsa.

Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne.

Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, "Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku. Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi."

Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun tafi haka kawai ba.

O tribunal de Cristo

Todos compareceremos diante do tribunal de Cristo para prestar contas. Cada um dará conta de si mesmo a Deus.

Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.

Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah. A rubuce yake cewa,

" Muddin ina raye,in ji Ubangiji,

kowace gwiwa za durƙusa a gabana;

kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ "

Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.

Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.

Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.

Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yi aiki mai kyau, ko kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi.

Shari’ar adalcin Allah

Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa.

Shari’ar adalcin Allah

Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?

Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su.

Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.

Rai ta wurin Ruhu

Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta yantar da ni daga Dokar Musa.

Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Deus é o juiz

O Senhor julgará o mundo com justiça. O juízo de Deus é verdadeiro e justo — Ele conhece todos os segredos do coração humano.

Ubangiji yana mulki har abada;

ya kafa kujerarsa don shari’a.

Ubangiji yana mulki har abada;

ya kafa kujerarsa don shari’a.

Zai hukunta duniya da adalci;

zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.

Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,

har da waɗanda aka yi a ɓoye,

ko nagari ne, ko mugu.

"Ina cikin dubawa,

"sai aka ajiye kursiyoyi,

sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.

Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;

gashin kansa sun yi fari kamar ulu.

Kursiyinsa kuma harshen wuta,

dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.

Kogin wuta yana gudu,

yana fitowa daga gabansa.

Dubun dubbai sun yi masa hidima;

dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa.

Aka zauna don shari’a,

aka kuma buɗe littattafai.

Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.

Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata.

Discernimento e graça

Temos um advogado junto ao Pai — Jesus Cristo. Não há condenação para os que estão em Cristo. Prove os espíritos.

Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.

Gwada ruhohi

Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

Kaiwa juna kotu

In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon kai ƙara a gaban tsarkaka? Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan! Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya! Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba?

Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan!

A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.

in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har zuwa ranar shari’a.

Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka?

Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari "I" naku zama "I". "A’a" naku kuma zama "A’a", don kada a hukunta ku.

Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. Gama shi da ya ce, "Kada ka yi zina," shi ne kuma ya ce, "Kada ka yi kisankai." In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da yanci,

Saboda haka kada ku bar wani shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci.

Saboda haka kada ku bar wani shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci. Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.

Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.

ba makamin da aka ƙera don cuce ki da zai yi nasara,

za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.

Wannan ne gādon bayin Ubangiji,

kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,"

in ji Ubangiji.

Raina yana marmarinka da dare;

da safe kuma raina yana son ganinka.

Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,

mutanen duniya kan koyi adalci.

Aure zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke,

amma Ubangiji yakan auna zuciya.

Yin abin da yake daidai da kuma nagari

Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.

Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.

Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,

bari zuciyarka kuma yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.

Ka bi shawarar zuciyarka

da kuma duk abin da idanunka suka gani,

amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan

Allah zai shari’anta ka.

Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan kasance da rai a cikin kansa. Ya kuma ba shi iko hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.

Ba wa waɗansu laifi

"Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-