Pular para o conteúdo
Publicidade

Lei

Por Bíblia Online

A lei de Deus é expressão do seu caráter e amor. Do Sinai ao Sermão do Monte, a lei orienta, protege e revela o padrão santo de Deus para a vida humana.

O propósito da lei

A lei de Deus revela o pecado e nos conduz a Cristo. Pela lei é que temos consciência do que é justo e do que é errado.

Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.

Bayi ga adalci

Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan!

Yancin mai bi

"Ana da dama a yi kome" sai dai ba kome ba ne yake da amfani. "Ana da dama a yi kome" sai dai ba kome ba ne mai ginawa.

Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, "Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.

Amar e obedecer

O maior mandamento é amar a Deus e ao próximo. Toda a lei se resume nestes dois mandamentos, que são o fundamento de tudo.

Na biyun ita ce, Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ba wata doka da ta fi waɗannan."

Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.

Ku yi ƙauna, gama ranar ta yi kusa

Kada hakkin kowa zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole ƙaunaci ɗan’uwansa.

Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan. Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.

Bênçãos da obediência à lei

Se andardes nos meus mandamentos, vivereis. A obediência à lei de Deus traz vida, paz e prosperidade espiritual.

Albarku don biyayya

In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya.

Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.

Ku ji tsoron Ubangiji

Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

Kada ka bar Littafin Dokokin nan rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.

Amma ku yi hankali, ku kiyaye umarnai da kuma dokokin da Musa bawan Ubangiji ya ba ku. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya kan hanyarsa, ku yi biyayya da umarnansa, ku riƙe shi sosai, ku bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku."

Na neme ka da dukan zuciyata;

kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

Na zaɓi hanyar gaskiya;

na sa zuciyata a kan dokokinka.

Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ya’yansu,

tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa

suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

Lei e graça

A lei veio para nos guiar; a graça veio para nos salvar. Em Cristo, cumprimos a lei pelo amor — o fruto do Espírito não tem lei contra si.

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,

adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!

Kada ku haɗa kai da marasa bi

Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

Seja o primeiro