Pular para o conteúdo
Publicidade

Língua

Por Bíblia Online

A língua tem poder de vida e de morte. A Bíblia compara a língua ao leme de um navio e à faísca que incendeia uma floresta. Dominar a língua é prova de maturidade espiritual.

O poder da língua

A morte e a vida estão no poder da língua. Quem a domina é varão perfeito, capaz de controlar todo o corpo.

Harshe yana da ikon rai da mutuwa,

kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.

Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya. Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so. Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.

Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. Yan’uwana, wannan bai kamata zama haka ba. Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi haifi ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba.

Palavras sábias

A língua branda quebra até ossos. A palavra certa no tempo certo é como maçãs de ouro em salvas de prata.

Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki,

magana mai hankali kan karye ƙashi.

Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi,

amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.

Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,

amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.

Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki,

amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

Disciplinar a fala

Quem guarda a boca e a língua guarda a sua alma de angústias. A religião sem controle da língua é vã.

In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.

Na ce, "Zan lura da hanyoyina

zan kuma kiyaye harshena daga zunubi;

zan sa linzami a bakina

muddin mugaye suna a gabana."

Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa

yana kuma so ga kwanaki masu kyau,

ka kiyaye harshenka daga mugunta

da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima,

harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.

Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa;

ƙafafunsa ba sa santsi.

Harshena zai yi zancen adalcinka

da kuma yabonka dukan yini.

Kafin in yi magana da harshena

ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

Ka cece ni, ya Ubangiji,

daga leɓuna masu ƙarya

da kuma daga harsuna masu yaudara.

Bari Ubangiji yanke dukan zaƙin bakinsu

da kuma kowane harshe mai fariya,

masu cewa,

"Da harsunanmu za mu yi nasara;

leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?"

Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,

gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.

Toda língua confessará

Ao nome de Jesus todo joelho se dobrará e toda língua confessará que Jesus Cristo é Senhor, para glória de Deus Pai.

Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

don a sunan Yesu kowace gwiwa za durƙusa,

a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

kowane harshe kuma furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

don ɗaukakar Allah Uba.

Ƙauna

In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.

Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka."

Sai Ubangiji ya sauko don ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. Ubangiji ya ce, "Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna."

Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

Seja o primeiro

Este artigo te tocou? Faça uma oração!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.