Maria
Maria, mãe de Jesus, é honrada nas Escrituras como a mulher escolhida por Deus para trazer ao mundo o Salvador. Sua fé, humildade e obediência são exemplo para todos os cristãos.
A escolhida de Deus
O anjo Gabriel anunciou a Maria que ela seria mãe do Filho do Altíssimo. Ela respondeu com fé: 'Faça-se em mim segundo a tua palavra.'
Annabcin haihuwar Yesu
A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. Mala’ikan ya je wurinta ya ce, "A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke."
Amma mala’ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba."
Haihuwar Yesu Kiristi
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
O Magnificat
Maria cantou: 'Minha alma engrandece ao Senhor!' Seu cântico exalta a misericórdia, o poder e a fidelidade de Deus.
Waƙar Maryamu
Sai Maryamu ta ce,
"Raina yana ɗaukaka Ubangiji
ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,
daga zamani zuwa zamani.
Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;
ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.
Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu
amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa
amma ya sallami mawadata hannu wofi.
Ya taimaki bawansa Isra’ila,
yana tunawa yă nuna jinƙai
ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,
kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu."
Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.
Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, "An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki."
Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, "Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka."
Sai ya ce, "Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?" Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.
Mãe fiel até o fim
Maria acompanhou Jesus desde o nascimento até a cruz. Ela estava entre os discípulos no Pentecostes, fiel em oração.
Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, "Ba su da sauran ruwan inabi."
Yesu ya ce, "Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna."
Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, "Ku yi duk abin da ya faɗa."
To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, "Mace, ga ɗanki," ga almajirin kuwa ya ce, "Ga mahaifiyarka." Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa
Sai mahaifiyar Yesu tare da ’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi. Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, "Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka."
Ya yi tambaya ya ce, "Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?"
Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, "Ga mahaifiyata da ’yan’uwana! Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata."
Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?"
Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.
Este artigo te tocou? Faça uma oração!
+581 estão orando agora.
Junte-se à corrente de oração.