Pular para o conteúdo
Publicidade

Marido e mulher

Por Bíblia Online

O casamento é aliança sagrada entre marido e mulher, instituída por Deus desde o Éden. A Bíblia define papéis complementares fundados em amor, respeito e fidelidade mútua.

Instituição divina

Deus criou homem e mulher e os uniu em uma só carne. O casamento é projeto divino que reflete o amor de Cristo pela Igreja.

Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

Miji da mace ya halicce su.

Ubangiji Allah ya ce, "Bai yi kyau mutumin kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi."

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Ya amsa ya ce, "Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ya yi su namiji da ta mace, ya kuma ce, Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda? Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum raba."

Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

Papéis no casamento

O marido ama e a mulher respeita. Ambos se submetem voluntariamente a Deus e um ao outro, em parceria e unidade.

Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. Kiristi ya yi haka don miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ciyar da shi, kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,

Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

Duk da haka, dole kowannenku ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar yi biyayya ga mijinta.

Umarnai don iyalan masu bi

Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

Matan aure da mazan Aure

Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.

Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu hana addu’oinku.

Fidelidade e união

O casamento é honroso e deve ser preservado com fidelidade. O cordão de três dobras não se rompe facilmente.

Biyu sun fi ɗaya,

gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

In ɗaya ya fāɗi,

abokinsa zai taimake shi tashi.

Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

ba shi kuma da wanda zai taimake shi tashi!

In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

mutum biyu za su iya kāre kansu.

Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

Wa yake iya samun mace mai halin kirki?

Darajarta ta fi ta lu’uluai.

Mijinta yana da cikakken amincewa da ita

kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.

Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,

amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne,

amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.

Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

bari mamanta su ishe ka kullum,

bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

Permanecer juntos

O que Deus uniu, o homem não separe. A Bíblia protege o casamento e orienta sobre convivência, perdão e perseverança conjugal.

Aure

To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum zauna ba aure. Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. Ya kamata miji cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma saki matarsa.

Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.

In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa je yaƙi, ko yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, faranta wa matar da ya aura rai.

Seja o primeiro