Mente
A mente é campo de batalha espiritual. A Bíblia nos chama a renovar o entendimento, pensar com sabedoria e buscar a mente de Cristo em todas as áreas da vida.
Amar a Deus com a mente
O maior mandamento inclui amar a Deus com toda a mente. A vida intelectual deve ser consagrada ao Senhor.
Yesu ya amsa ya ce, " ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.
Sabedoria e discernimento
A sabedoria é melhor que rubis. Quem a encontra, encontra a vida. A mente sábia discerne, planeja e previne erros.
Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,
mutumin da ya sami fahimi,
Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa;
duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe
haka mutum kan koyi daga mutum.
Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,
amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,
da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.
Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce,
marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
Construir sobre a rocha
Quem ouve as palavras de Jesus e as pratica é como o sábio que edificou sobre a rocha firme e inabalável.
Magini mai hikima da marar hikima
"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
Hikima iri biyu
Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima.
Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.