Pular para o conteúdo
Publicidade

Messias

Por Bíblia Online

Jesus é o Messias prometido — o Cristo, o Ungido de Deus. Séculos de profecias apontaram para Ele, e Pedro declarou: 'Tu és o Cristo, o Filho do Deus vivo.'

A confissão messiânica

Pedro confessou: Tu és o Cristo, o Filho do Deus vivo. Os apóstolos pregaram incansavelmente que Jesus é o Messias prometido.

Ya tambaye su, "Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?"

Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai."

Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

Amma na sami taimakon Allah har zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru, cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai."

As profecias cumpridas

O Messias viria como Príncipe da Paz, Salvador e Senhor. Cada profecia se cumpriu em Jesus de Nazaré, nascido em Belém.

Gama a gare mu an haifa mana yaro,

a gare mu an ba da ɗa,

gwamnati za kasance a kafaɗarsa.

Za a ce da shi

Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

Uban Madawwami, Sarkin Salama.

Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.

Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.

Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za ba.

Seja o primeiro