Milagres de Jesus
Os Evangelhos registram dezenas de milagres realizados por Jesus — curas, ressurreições, domínio sobre a natureza e libertações. Cada milagre revelava sua divindade e compaixão.
Curas de cegos e surdos
Jesus devolveu a visão aos cegos e a audição aos surdos, manifestando seu poder sobre toda enfermidade e deficiência.
Yesu ya warkar da makafi da kuma kurame
Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, "Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!"
Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, "Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?"
Suka amsa suka ce, "I, Ubangiji."
Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, "Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka"; sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, "Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan." Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.
Makafi biyu sun sami ganin gari
Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, "Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!"
Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, "Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!"
Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, "Me kuke so in yi muku?"
Suka amsa suka ce, "Ubangiji, muna so mu sami ganin gari."
Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
An warkar da makaho
Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, "Kana iya ganin wani abu?"
Sai ya ɗaga kai ya ce, "Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya."
Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai. Yesu ya sallame shi gida ya ce, "Kada ka shiga cikin ƙauyen."
Warkar da kurma wanda yake kuma bebe
Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis. A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.
Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, "Effata!" (Wato, "Buɗe!"). Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.
Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. Mutane suka cika da mamaki, suka ce, "Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana."
Bartimawus makaho ya sami gani
Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, "ɗan Timawus"), yana zaune a gefen hanya yana bara. Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, "Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, "Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
Yesu ya tsaya ya ce, "Ku kira shi."
Sai suka kira makahon suka ce, "Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka." Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.
Yesu ya tambaye shi ya ce, "Me kake so in yi maka?"
Makahon ya ce, "Rabbi, ina so in sami ganin gari."
Yesu ya ce, "Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
Makaho mai bara ya sami ganin gari
Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. Suka ce masa, "Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa."
Sai ya yi kira ya ce, "Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, "Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, "Me kake so in yi maka?"
Sai ya amsa ya ce, "Ubangiji, ina so in sami ganin gari."
Yesu ya ce masa, "Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.
Yesu ya warkar da mutumin da aka haifa makaho
Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, "Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?"
Sai Yesu ya ce, "Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya."
Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. Ya ce masa, "Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam" (kalman nan tana nufin "Aikakke"). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
Curas de paralíticos e enfermos
Paralíticos caminharam, leprosos ficaram limpos e todo tipo de doença foi curada pelo toque e pela palavra de Jesus.
Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, "Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni."
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, "Ina so, ka tsabtacce!" Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa. Sai Yesu ya ce masa, "Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su."
Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka."
Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, "Wannan mutum yana yin saɓo!"
Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, "Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida." Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, "Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?"
Ya ce musu, "In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci."
Sa’an nan ya ce wa mutumin, "Miƙa hannunka." Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
Mutum mai kuturta
Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, "In kana so, za ka iya tsabtacce ni."
Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, "Na yarda, ka tsabtacce!" Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.
Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Saurayi, an gafarta zunubanka."
To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, "Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?"
Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, "Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida." Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, "Ba mu taɓa ganin abu haka ba!"
Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, "Tashi ka tsaya a gaban kowa."
Sai Yesu ya tambaye su ya ce, "Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?" Amma suka yi shiru.
Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, "Miƙo hannunka." Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
Warkar da kuturu
Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, "Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni."
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, "Na yarda, ka zama da tsabta!" Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu. Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, "Saurayi, an gafarta maka zunubanka."
Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, "Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?"
Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, "Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku? Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida." Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, "Tashi ka tsaya a gaban kowa." Sai ya tashi ya tsaya.
Yesu ya ce musu, "Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?"
Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, "Miƙo hannunka." Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
Bangaskiyar jarumin Roma
Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum. A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, "Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu." Sai Yesu ya tafi tare da su.
Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, "Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi."
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, "Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba." Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.
a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, "Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki." Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
Yesu a gidan Bafarisiye
Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, "Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?" Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.
An warkar da kutare goma
Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, suka yi kira da babbar murya, suka ce, "Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!"
Da ya gan su sai ya ce, "Ku je ku nuna kanku ga firistoci." Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.
Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
Yesu ya yi tambaya ya ce, "Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?" Sai ya ce masa, "Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai."
Warkarwa a tafki
Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, "Kana so ka warke?"
Marar amfanin nan ya ce, "Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni."
Sai Yesu ya ce masa, "Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya." Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.
A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,
Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
Yesu ya ce masa, "Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya."
Ma’aikacin hukuman ya ce, "Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu."
Sai Yesu ya amsa ya ce, "Ka tafi. Ɗanka zai rayu."
Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, "Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai."
Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, "Ɗanka zai rayu." Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.
A mulher com fluxo de sangue
Uma mulher que sofria há doze anos tocou a orla do manto de Jesus e foi curada instantaneamente pela sua fé.
A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa. Ta ce a ranta, "Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke."
Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, "Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke." Nan take macen ta warke.
A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, domin ta yi tunani cewa, "Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke." Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
Yesu ya yi tambaya, "Wa ya taɓa ni?"
Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, "Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe."
Amma Yesu ya ce, "Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina."
Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. Sai Yesu ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya."
Ressurreições
Jesus ressuscitou mortos — a filha de Jairo, o filho da viúva de Naim e Lázaro. Ele é Senhor sobre a morte.
Yarinya da ta mutu da kuma mace marar lafiya
Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, "Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu." Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.
Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya, sai ya ce, "Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne." Amma suka yi masa dariya. Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.
Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa, ya roƙe shi da gaske ya ce, "Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu." Sai Yesu ya tafi tare da shi.
Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.
Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. Sai ya shiga ciki, ya ce musu, "Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi." Sai suka yi masa dariya.
Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take. Sai ya kama hannunta ya ce mata, "Talita kum!" (Wato, "Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!"). Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai.
Yesu ya ci gaba da cewa, "To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,
" ‘Mun busa muku sarewa,
amma ba ku yi rawa ba,
Mun kuma yi muku waƙar makoki,
ba ku kuma yi kuka ba.’
Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta."
Mace mai zunubi ta shafe wa Yesu turare
To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta,
Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe.
Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, "Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu."
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita."
Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, "Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne."
Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, "Diyata, tashi." Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.
Mutuwar Lazarus
To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, "Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya."
Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, "Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan." Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
Sai ya ce wa almajiransa, "Mu koma Yahudiya."
Sai suka ce, "Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?"
Yesu ya amsa ya ce, "Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske."
Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, "Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi."
Almajiransa suka ce, "Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi." Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, "Lazarus ya mutu,
Domínio sobre a natureza
Jesus acalmou a tempestade, andou sobre as águas e multiplicou pães. A natureza obedece à voz do seu Criador.
Yesu ya kwantar da hadari
Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, "Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!"
Ya amsa ya ce, "Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?" Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
Mutanen suka yi mamaki suka ce, "Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!"
Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, "Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci."
Yesu ya amsa, "Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci."
Suka ce, "Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan."
Ya ce, "Ku kawo mini su a nan." Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.
Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, "Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya."
Sai almajiransa suka amsa suka ce, "Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?"
Yesu ya tambaye su, "Burodi guda nawa kuke da shi?"
Suka amsa suka ce, "Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye."
Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.
Harajin haikali
Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, "Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?"
Ya amsa ya ce "I, yana biya."
Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, "Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?"
Bitrus ya amsa ya ce, "Daga wurin waɗansu."
Yesu ya ce masa, "Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan. Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan."
Itacen ɓaure ya yanƙwane
Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, "Kada ka ƙara yin ’ya’ya!" Nan da nan itacen ya yanƙwane.
Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, "Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?"
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a."
Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, "Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?"
Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, "Shiru! Ku natsu!" Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.
Sai ya ce wa almajiransa, "Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?"
Suka tsorata, suka ce wa juna, "Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!"
A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, "Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci."
Sai ya amsa ya ce, "Ku, ku ba su wani abu su ci."
Suka ce masa, "Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?"
Sai ya yi tambaya ya ce, "Burodi nawa kuke da su? Je ku duba."
Da suka duba, sai suka ce, "Biyar da kifi biyu."
Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.
Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.
Nan da nan ya yi magana da su ya ce, "Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro." Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,
Yesu ya ciyar da dubu huɗu
A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce, "Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci. In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa."
Almajiransa suka amsa suka ce, "Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?"
Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, "Burodi guda nawa kuke da su?"
Suka ce, "Bakwai."
Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka. Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,
Yesu ya tsabtacce haikali
Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. Sai ya ce wa itacen, "Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka." Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
Itacen ɓaure da ya yanƙwane
Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, "Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!"
Yesu ya amsa ya ce, "Ku gaskata da Allah. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku."
Kiran almajirai na farko
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah, sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu. Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, "Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi."
Siman ya amsa ya ce, "Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin."
Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, "Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!" Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki.
Sai Yesu ya ce wa Siman, "Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne." Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
Yesu ya kwantar da ruwa da iska
Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, "Mu haye zuwa wancan gefen tafkin." Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, "Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!"
Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. Sai ya tambayi almajiransa, "Ina bangaskiyarku?"
A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, "Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?"
Yesu ya kwantar da ruwa da iska
Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, "Mu haye zuwa wancan gefen tafkin." Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, "Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!"
Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. Sai ya tambayi almajiransa, "Ina bangaskiyarku?"
A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, "Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?"
Warkar da mai aljanu
Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili.
Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, "Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa."
Yesu ya ce, "Ku, ku ba su wani abu su ci."
Sai suka ce masa, "Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron." Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar.
Amma ya ce wa almajiransa, "Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin." Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna. Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.
Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, "Ba su da sauran ruwan inabi."
Yesu ya ce, "Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna."
Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, "Ku yi duk abin da ya faɗa."
Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
Sai Yesu ya ce wa bayin, "Ku ciccika tulunan da ruwa." Suka kuwa ciccika su fal.
Sa’an nan ya ce musu, "Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin."
Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, "Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu."
Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
Sai Filibus ya amsa ya ce, "Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!"
Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana, "Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan."
Yesu ya ce, "Ku sa mutanen su zauna." Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar. Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, "Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace." Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata. Amma ya ce musu, "Ni ne; kada ku ji tsoro." Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
Yesu da kamun kifin banmamaki
Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. Sai Siman Bitrus ya ce musu, "Za ni kamun kifi," suka ce, "Za mu tafi tare da kai." Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
Sai ya ce musu, "Abokai, kuna da kifi kuwa?"
Suka amsa suka ce, "A’a."
Ya ce musu, "Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu." Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, "Ai, Ubangiji ne!" Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, "Ai, Ubangiji ne," sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
Yesu ya ce musu, "Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu." Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.
Libertações
Jesus expulsou demônios com autoridade. Os espíritos impuros não resistiam à sua palavra e saíam imediatamente.
Bangaskiyar jarumi
Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. Ya ce, "Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai."
Yesu ya ce masa, "Zan je in warkar da shi."
Jarumin ya amsa, "Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi."
Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, "Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba. Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora."
Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, "Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka." A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
Warkar da mutum biyu masu aljanu
Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. Suka yi ihu suka ce, "Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?" Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?
Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, "In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan."
Ya ce musu, "Ku tafi!" Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.
Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana. Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, "Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba."
Yesu da Be’elzebub
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
Bangaskiyar mutuniyar Kan’ana
Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon. Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, "Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta."
Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, "Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu."
Ya amsa ya ce, "An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai."
Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, "Ubangiji, ka taimake ni!"
Ya amsa ya ce, "Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu."
Ta amsa, ta ce, "I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu."
Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, "Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki." ’Yarta kuwa ta warke nan take.
Warkarwar yaro mai aljani
Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya ce, "Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba."
Yesu ya amsa ya ce, "Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan." Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, "Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!"
Yesu ya tsawata masa ya ce, "Yi shiru! Fita daga cikinsa!" Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
Warkar da mai aljanu
Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai.
Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya yi ihu da babbar murya ya ce, "Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!" Gama Yesu ya riga ya ce masa, "Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!"
Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, "Mene ne sunanka?"
Sai ya amsa ya ce, "Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa." Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin.
A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, "Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu." Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru.
Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa."
Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, "Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi."
Bangaskiyar Baheleniya
Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.
Yesu ya ce mata, "Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu."
Ta amsa, ta ce, "I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara."
Sai ya ce mata, "Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki."
Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, "Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba."
Yesu ya ce, "Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron."
Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.
Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, "Tun yaushe yake haka?"
Ya ce, "Tun yana ƙarami. Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu."
Yesu ya ce, " ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata."
Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, "Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!"
Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, "Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa."
Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, "Ai, ya mutu." Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
Yesu ya warkar da mutane da yawa
Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta. Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima.
Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, "Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!" Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
Yesu ya tambaye shi, "Mene ne sunanka?"
Sai ya amsa, "Tuli," gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis.
A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
"Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah."
Sāke kamanni
Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a. Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya. Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima.
Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi. Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya." (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)
Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, "Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba."
Yesu ya amsa ya ce, "Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan."
Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa. Duk suka yi mamakin girman Allah.
Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,
Yesu da Be’elzebub
Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.
Sai ɗayansu ya kai sara ga bawan babban firist, ya sare kunnen damansa.
Amma Yesu ya amsa ya ce, "Kada a ƙara yin wannan!" Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.
Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, "Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa,
" ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka,
wanda zai shirya hanya, a gabanka.’
Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi."
(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)