Publicidade

Morte de Jesus

Por Bíblia Online

A morte de Jesus é o sacrifício supremo do amor de Deus. Na cruz, o Cordeiro de Deus carregou os pecados do mundo, satisfez a justiça divina e abriu o caminho da salvação para todos.

O sacrifício na cruz

Jesus disse: 'Está consumado!' Na cruz, Ele cumpriu toda a lei, pagou o preço do pecado e reconciliou a humanidade com Deus.

Mutuwar Yesu

Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, "Ina jin ƙishirwa." To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, "An gama." Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.

Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.

Sai suka ce wa juna, "Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci."

Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,

"Suka rarraba tufafina a junansu,

suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata."

Abin da sojojin suka yi ke nan.

To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, "Mace, ga ɗanki," ga almajirin kuwa ya ce, "Ga mahaifiyarka." Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

Da suka isa wurin da ake kira "Ƙoƙon Kai," nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Yesu ya ce, "Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba." Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, "Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe."

Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. Suka ce, "In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana."

Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce,

Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, "Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!"

Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, "Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba."

Sai ya ce, "Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka."

Yesu ya amsa, ya ce masa, "Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama."

Mutuwar Yesu

Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, "Eloi, Eloi, lama sabaktani?" (Wato, "Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?").

A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, "Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!"

Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,

aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;

hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,

kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,

kowannenmu ya kama hanyarsa;

Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa

hukuncin da ya wajaba a kanmu.

Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba,

duk da haka bai buɗe bakinsa ba;

aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka,

kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru,

haka bai buɗe bakinsa ba.

Karnuka sun kewaye ni;

ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka,

sun soki hannuwana da ƙafafuna.

Zan iya ƙirga ƙasusuwana;

mutane suna farin ciki a kaina.

Sun raba rigunana a tsakaninsu

suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.

Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a;

suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,

"Ya dogara ga Ubangiji;

bari Ubangiji cece shi.

Bari cece shi,

da yake yana jin daɗinsa."

O amor que se entrega

Ninguém tem maior amor do que aquele que dá a vida pelos amigos. Deus prova seu amor em que Cristo morreu por nós quando ainda éramos pecadores.

Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada hallaka sai dai sami rai madawwami.

Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin yan’uwanmu.

Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

Aka kuma same shi a kamannin mutum,

ya ƙasƙantar da kansa

ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,

mutuwar ma ta gicciye!

Morte e ressurreição

Jesus morreu e ressuscitou, e a morte não mais tem domínio sobre Ele. Pelo batismo, participamos de sua morte e ressurreição.

Gama mun san cewa da yake an da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah.

Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don ɗauki zunubi ba, sai dai don kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

"Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

"Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.

Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har dawo.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-