A mulher virtuosa
A mulher virtuosa de Provérbios 31 é um retrato de excelência. Seu valor excede o de rubis — ela é sábia, trabalhadora, generosa e teme ao Senhor acima de tudo.
Uma joia rara
Mulher virtuosa, quem a achará? Seu valor excede o de rubis. Ela é o coração da família e a força do lar.
Wa yake iya samun mace mai halin kirki?
Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
Wa yake iya samun mace mai halin kirki?
Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.
Mijinta yana da cikakken amincewa da ita
kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.
Takan yi masa alheri ba mugunta ba,
dukan kwanakin ranta.
Takan zaɓi ulu da lilin
ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.
Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne
tana kawo abincinta daga nesa.
Takan farka tun da sauran duhu;
ta tanada wa iyalinta abinci
ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;
daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;
hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,
kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
Da hannunta take riƙe abin kaɗi
ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.
Takan marabci talakawa
takan kuma taimaki masu bukata.
Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne,
amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
Yanzu kuwa ’yata kada ki ji tsoro. Zan yi miki dukan abin da kika roƙa. Dukan ’yan’uwana na gari sun san cewa ke mace ce mai halin kirki.
Caráter acima da aparência
Enganosa é a graça e vã é a formosura, mas a mulher que teme ao Senhor será louvada. A verdadeira beleza é interior.
Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.
Mace mai hikima kan gina gidanta,
amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,
amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.