Namoro e sexo
Namoro e sexo são temas que a Bíblia trata com clareza e sem tabus. Deus criou o sexo como bênção dentro do casamento e nos chama à pureza fora dele.
Pureza sexual
A vontade de Deus é a santificação. Cada um saiba controlar seu próprio corpo em santidade e honra, não na paixão do desejo.
Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
"An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci." Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.
Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
Arrependimento e restauração
Bem-aventurado aquele cujo pecado é perdoado. Deus restaura os que se arrependem e cria neles um coração limpo e renovado.
Mai farin ciki ne shi
wanda aka gafarta masa laifofinsa,
wanda aka shafe zunubansa.
Mai farin ciki ne mutumin
da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa
wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
Sa’ad da na yi shiru,
ƙasusuwana sun yi ta mutuwa
cikin nishina dukan yini.
Gama dare da rana
hannunka yana da nauyi a kaina;
an shanye ƙarfina ƙaf
sai ka ce a zafin bazara. Sela
Sa’an nan na furta zunubina a gare ka
ban kuwa ɓoye laifina ba.
Na ce, "Zan furta
laifofina ga Ubangiji."
Ka kuwa gafarta
laifin zunubina. Sela
Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka
yayinda kake samuwa;
tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,
ba za su kai wurinsa ba.
Ka wanke dukan kurakuraina
ka tsarkake ni daga zunubina.
Gama ina sane da laifofina
zunubaina kuma kullum suna a gabana.
Kai kaɗai na yi wa zunubi
na yi abin da yake mugu a idonka,
ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana
aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;
ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
Bari in ji farin ciki da murna;
bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina
ka kuma shafe dukan kurakuraina.
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,
ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
Kada ka fid da ni daga gabanka
ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
Ka mayar mini farin cikin cetonka
ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.