Não desista!
'Não desista!' é o grito do céu para a terra. Deus nos encoraja a perseverar na fé, na oração e na esperança, porque a vitória pertence aos que não se rendem.
Força na fraqueza
Os que esperam no Senhor renovam as forças. Deus não se cansa nem se fatiga — Ele dá poder aos fracos e vigor aos cansados.
Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.
Mai Ceto kaɗai na Isra’ila
To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
"Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
Perseverança na fé
Não perca a confiança, pois ela tem grande recompensa. O justo viverá pela fé, e quem perseverar até o fim será salvo.
Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.
Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.
Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.
Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
Deus é refúgio
O Senhor é nosso refúgio e fortaleza. Ele ouve nossas orações, nos consola nas tribulações e transforma choro em dança.
Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
Waɗanda suka yi shuka da hawaye
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
Shi da ya fita yana kuka,
riƙe da iri don shuki,
zai dawo da waƙoƙin farin ciki,
ɗauke da dammuna.
Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,
dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.
Maganarka fitila ce ga ƙafafuna
haske kuma a kan hanyata.
Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
Vitória em Cristo
Jesus venceu o mundo e nos dá vitória. Para Deus nada é impossível, e Ele faz infinitamente mais do que pedimos ou pensamos.
"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."
Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, "Ku ma za ku tafi ne?"
Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah."
Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
Roƙa, nema, ƙwanƙwasa
"Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne."
Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."
Gama ba abin da zai gagari Allah."
Esperança e transformação
O Senhor completa a boa obra que começou em nós. Ele faz novas todas as coisas e dá esperança para o futuro.
da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Sabuwar sama da sabuwar duniya
Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, "Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe."
Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku."
Permanecendo firme
Persevere na oração, firme-se na Palavra e fortaleça-se na graça de Cristo. A fé vem pelo ouvir, e o ouvir pela Palavra de Deus.
Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, "Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka," in ji Ubangiji.
Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.
Fiye da masu nasara
Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.
Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.