Não temas
'Não temas' é uma das frases mais repetidas na Bíblia. Deus a pronuncia nos momentos de maior temor, lembrando que sua presença e poder são maiores que qualquer ameaça.
Deus está contigo
Não temas, porque eu sou contigo. Deus repete essa promessa em cada crise, guerra e desafio que seus filhos enfrentam.
Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,
ya ƙaramin Isra’ila,
gama ni kaina zan taimake ka," in ji Ubangiji,
Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona,
ka haura a bisa dutse.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima,
ka tā da muryarka ka yi ihu,
ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro;
faɗa wa garuruwan Yahuda,
"Ga Allahnku!"
Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."
Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,
"Kada ka ji tsoro, Abram.
Ni ne garkuwarka,
kuma ladanka zai zama mai girma."
Coragem diante do perigo
Não tenhas medo — o Senhor teu Deus está no meio de ti, poderoso para salvar. Ele luta por nós e dá forças aos medrosos.
A wannan rana za su cewa Urushalima,
"Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;
kada ki bar hannuwanki su raunana.
Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa."
Sai annabin ya ce, "Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su."
Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, "Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!" Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha.
Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;
ki yi murna ki kuma yi farin ciki.
Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.
Amma Ubangiji ya ce mini, "Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka," in ji Ubangiji.
Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, "Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru. Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni."
Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye. Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne.
Fé que vence o medo
O medo não vem de Deus. Jesus disse: não temas, crê somente! A fé dissipa o medo e nos conecta ao poder de Deus.
Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai."
Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.
Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.
Amma mala’ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, "Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!"