Nascer de novo
Nascer de novo é a porta de entrada para a vida em Deus. Jesus ensinou que sem o novo nascimento espiritual, ninguém pode ver nem entrar no Reino de Deus.
A necessidade do novo nascimento
Jesus declarou a Nicodemos: 'Aquele que não nascer de novo não pode ver o Reino de Deus.' O novo nascimento é pelo Espírito.
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa."
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa."
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, "Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!"
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu."
Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba."
Mafi girma a mulkin sama
A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, "Wane ne mafi girma a mulkin sama?"
Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.
Nova criação em Cristo
Quem está em Cristo é nova criação. Morremos e ressuscitamos com Ele para viver em novidade de vida, livres do velho homem.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.
In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan.
Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.
Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
Filhos de Deus
Nascemos de novo pela Palavra viva de Deus. Quem crê em Jesus recebe o direito de se tornar filho de Deus, nascido do Espírito.
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
Yabo ga Allah domin bege mai rai
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,
Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.
Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.
Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.
Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.