Publicidade

Nascimento

Por Bíblia Online

O nascimento é obra das mãos de Deus. Cada criança é formada por Ele no ventre materno com propósito e amor. A Bíblia celebra a vida desde a concepção até a eternidade.

O nascimento de Jesus

O maior nascimento da história mudou o curso da humanidade. Jesus nasceu de uma virgem pelo poder do Espírito Santo, conforme as profecias.

Haihuwar Yesu Kiristi

Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so ba ta kunya, tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani sake ta a ɓoye.

Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. Za haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu."

Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, "Ga shi budurwa za yi ciki, za haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel" (wanda yake nufin "Allah tare da mu").

Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.

Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za yi ciki, za haifi ɗa, za kuwa kira shi Immanuwel.

Annabcin haihuwar Yesu

A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.

Amma mala’ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba."

Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, "Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?"

Mala’ikan ya amsa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

Formados desde o ventre

Deus nos teceu no ventre de nossa mãe. Antes de nascermos, Ele já nos conhecia e nos separou para um propósito sagrado.

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

sa’ad da aka yi ni asirce.

Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

Idanunka sun ga jikina marar fasali;

dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

kafin ɗayansu kasance.

"Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,

kafin a haife ka, na keɓe ka;

na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai."

Duk da haka ka fitar da ni daga ciki;

ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.

Daga haihuwa an jefa ni a kanka;

daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.

Daga haihuwa na dogara gare ka;

kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.

Kullayaumi zan yabe ka.

"Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

Mai yiwuwa ta manta,

amma ba zan taɓa manta da ke ba!

Zan kai mace har haihuwa

in kuma sa ta kāsa haihu?" In ji Ubangiji.

"Zan rufe mahaihuwa

sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?" In ji Allahnku.

Crianças — bênção e promessa

Jesus acolheu as crianças e disse: delas é o Reino dos céus. Os filhos são herança do Senhor e motivo de alegria para os pais.

Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."

Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.

Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.

Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji;

na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.

Nascer de novo

Jesus ensinou que é preciso nascer de novo para ver o Reino de Deus. O novo nascimento é espiritual — pelo Espírito e pela Palavra.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa."

Macen da za haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.

Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.

Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-