Pular para o conteúdo
Publicidade

Nem só de pão vive o homem

Por Bíblia Online

'Nem só de pão vive o homem' — essa declaração de Jesus ao diabo no deserto revela que a Palavra de Deus é o verdadeiro alimento que sustenta a vida em plenitude.

O verdadeiro alimento

Quando tentado a transformar pedras em pão, Jesus respondeu com a Escritura: a vida humana depende de toda palavra que sai da boca de Deus.

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake cewa, Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah."

Iblis ya ce masa, "In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse zama burodi."

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake, Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba."

Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.

Jesus, o pão vivo

Jesus é o pão da vida que desceu do céu. Quem come deste pão viverá para sempre. Ele é o sustento que satisfaz a fome da alma.

Sa’an nan Yesu ya furta cewa, "Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.

Ni ne burodin rai.

Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai."

Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada."

Buscar o Reino acima de tudo

Não andeis ansiosos pelo que comer ou beber. Buscai primeiro o Reino de Deus, e todas estas coisas vos serão acrescentadas.

Kada ku damu

"Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?

Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. Gama duniya da ba san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.

Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, "Rabbi, ci abinci mana."

Amma ya ce musu, "Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba."

Sai almajiran suka ce wa juna, "Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?"

Yesu ya ce, "Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.

Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,

ba kuma ya’ya a kuringar inabi,

ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,

gonaki kuma ba su ba da abinci ba,

ko da yake babu tumaki a garke,

ba kuma shanu a turaku,

duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,

zan yi murna da Allah Mai Cetona.

Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina;

yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa,

yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi.

Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.

Seja o primeiro