Nova aliança
A Nova Aliança é o pacto de graça que Deus estabeleceu através de Jesus Cristo. Diferente da antiga, ela é escrita no coração, mediada pelo sangue de Cristo e acessível a todos.
A profecia da Nova Aliança
Jeremias profetizou uma aliança nova em que Deus escreveria sua lei no coração do povo. Essa promessa se cumpriu em Cristo.
"Lokaci yana zuwa," in ji Ubangiji,
"sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
Ba zai zama kamar alkawarin
da na yi da kakanni kakanninsu ba
sa’ad da na kama su da hannu
na bishe su daga Masar,
domin sun take alkawarina,
ko da yake na zama miji a gare su,"
in ji Ubangiji.
"Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila
bayan wannan lokaci," in ji Ubangiji.
"Zan sa dokata a tunaninsu
in kuma rubuta ta a zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
za su kuma zama mutanena.
Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,
ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin duk za su san ni,
daga ƙaraminsu har zuwa babba,"
in ji Ubangiji.
"Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba."
Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.
Ta wurin kira wannan alkawari "sabo," ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.
Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
Selada com sangue
Jesus instituiu a Nova Aliança na Última Ceia: 'Este cálice é a nova aliança no meu sangue.' Seu sacrifício é definitivo e perfeito.
Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, "Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.
Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, "Ku shassha daga cikinsa, dukanku. Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.
Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. Ya ce, "Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye."
Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.
Reconciliação e vida nova
Pela Nova Aliança somos reconciliados com Deus, trazidos para perto pelo sangue de Cristo e feitos embaixadores da reconciliação.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.
Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu "kaciya" sukan kira ku "marasa kaciya" (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.