Pular para o conteúdo
Publicidade

Obediência aos pais

Por Bíblia Online

A obediência aos pais é mandamento divino com promessa de vida longa. A Bíblia valoriza a honra filial e ensina os filhos a respeitar e obedecer aos pais com amor.

Honrar pai e mãe

O quinto mandamento ordena honrar pai e mãe. É o primeiro mandamento com promessa: para que vá bem e vivas muito na terra.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Gama Allah ya ce, Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Obedecer e respeitar

Filhos, obedecei a vossos pais no Senhor. A obediência filial é expressão de amor e temor a Deus.

Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Za su zama kayan ado don su inganta ka

da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

Gargaɗi a kan zina

Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;

ka ɗaura su kewaye da wuyanka.

Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;

sa’ad da kake barci, za su lura da kai;

sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.

Gama waɗannan umarnai fitila ne,

wannan koyarwa haske ne,

kuma gyare-gyaren horo

hanyar rayuwa ce,

Hikima ce mafi girma duka

Ku saurara ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

ku mai da hankali, ku sami fahimi.

Ina ba ku sahihiyar koyarwa,

saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,

yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

ya koya mini ya ce,

"Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;

ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;

kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

Kada ka ƙyale hikima, za kuwa tsare ka;

ka ƙaunace ta, za kuwa lura da kai.

Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,

amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Disciplina e consequências

A vara e a repreensão dão sabedoria. A Bíblia adverte sobre as consequências sérias da rebeldia e desonra aos pais.

Sandar gyara kan ba da hikima,

amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.

Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa

ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.

"Idon da yake yi wa mahaifi ba’a,

wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya,

hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido,

ungulai za su cinye su.

"Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

Gagararren ɗa

In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. Za su ce wa dattawan, "Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi." Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.

In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,

fitilarsa za mutu a tsakiyar duhu.

Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

Amma in gwauruwa tana da ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

Seja o primeiro