Publicidade

Orgulho

Por Bíblia Online

O orgulho é um dos pecados mais condenados na Bíblia. Deus resiste aos soberbos, mas dá graça aos humildes. A humildade é o caminho da honra verdadeira.

Deus resiste ao soberbo

A soberba precede a ruína e o orgulho antecede a queda. Deus abomina o coração altivo e promete humilhar quem se exalta.

Girmankai yakan zo kafin hallaka,

girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.

Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai.

Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.

Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum,

amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.

Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;

ina ƙin girman kai da fariya,

halin mugunta da kuma muguwar magana.

Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,

amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.

Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo,

amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.

Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci

amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.

Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci

amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.

Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,

amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,

amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai

amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.

Humildade como caminho

Humilhai-vos diante do Senhor e Ele vos exaltará. A grandeza no Reino vem pelo serviço humilde, não pela autopromoção.

Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

"Allah yana gāba da masu girman kai

amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u."

Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.

Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

"Allah yana gāba da mai girman kai,

amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai."

Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi."

Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai kula da sha’anin waɗansu ma.

A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

Os perigos do orgulho

O orgulho cega, gera contendas e afasta de Deus. A Escritura adverte contra a soberba da vida e a vã glória mundana.

Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-shaawacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.

Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!

In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.

Amma, "Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji." Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

Ya ci gaba, "Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum."

Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,

amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

Sauƙinkai da tsoron Ubangiji

sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.

Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.

O olhar de Deus

O Senhor não olha como o homem. Ele vê o coração e se agrada dos quebrantados de espírito e dos que tremem diante da sua Palavra.

Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, "Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya."

"Ka daina maganganu na girman kai

ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai;

gama Ubangiji Allah ne masani

daga gare shi kuma ana auna ayyuka.

Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,

ta haka suka kasance?"

In ji Ubangiji.

"Wannan mutum ne nake jin daɗi,

shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,

yana kuma rawar jiki ga maganata.

Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.

Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, "Ku faɗa masa, Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ "

Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Seja o primeiro
Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-29_22-07-56-