Pular para o conteúdo
Publicidade

Paciência

Por Bíblia Online

A paciência é fruto do Espírito e virtude essencial da vida cristã. Deus é paciente conosco, e nos chama a ser pacientes com os outros e nas provações.

A paciência de Deus

Deus é clemente e tardio em irar-se. Sua paciência revela seu desejo de que todos se arrependam e cheguem ao conhecimento da verdade.

Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani hallaka, sai dai kowa kai ga tuba.

Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.

Ku kyakkece zuciyarku

ba rigunanku ba.

Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

yakan kuma janye daga aika da bala’i.

Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.

Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

ya tashi don nuna muku jinƙai.

Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.

Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

Esperar com paciência

Os que esperam no Senhor renovam as forças. A paciência produz caráter, e o caráter produz esperança que não decepciona.

Ka dogara ga Ubangiji,

ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya

ka kuma dogara ga Ubangiji.

Ka natsu a gaban Ubangiji

ka kuma jira da haƙuri gare shi;

kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

in kuma jira da sa zuciya.

Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.

Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum."

Paciência nas provações

O amor é paciente. A paciência é marca de maturidade espiritual e nos permite perseverar mesmo quando as circunstâncias são adversas.

Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,

Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.

Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.

Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa.

Perseverança até o fim

Quem perseverar até o fim será salvo. O domínio próprio é maior que a conquista de uma cidade.

amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

"Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.

Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi,

ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa,

amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.

Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

amma alherinsa har matuƙa ne;

mai yiwuwa a yi kuka da dare

amma farin ciki kan zo da safe.

Seja o primeiro