Pular para o conteúdo
Publicidade

Pais e filhos

Por Bíblia Online

A relação entre pais e filhos é uma das mais preciosas na Bíblia. Deus estabeleceu a família como escola de fé, amor e formação de caráter.

Honrar pai e mãe

Honrar os pais é o primeiro mandamento com promessa. Os filhos são chamados a obedecer, respeitar e cuidar de seus pais.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."

Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

Faɗi 17

Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,

kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa

ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.

In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa,

fitilarsa za mutu a tsakiyar duhu.

Amma in gwauruwa tana da ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

Instruir os filhos

Os pais devem instruir os filhos no caminho certo. A educação começa cedo, com disciplina amorosa e ensino constante da Palavra.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Za su zama kayan ado don su inganta ka

da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

Sandar gyara kan ba da hikima,

amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.

Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,

amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.

Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

Filhos como bênção

Os filhos são herança do Senhor. A coroa dos velhos são os filhos dos filhos, e a glória dos filhos são seus pais.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ya’yansu.

Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

Karin maganar Solomon.

Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,

amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

"Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!"

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Ba za a kashe iyaye a maimakon ya’yansu ba, ba kuwa za a kashe ya’ya a maimakon iyayensu ba; kowa ya yi zunubi, shi za a kashe.

Seja o primeiro