Paixão
A Bíblia nos chama a dominar as paixões e desejos da carne. O cristão é chamado a viver pelo Espírito, crucificando as obras da carne e buscando a santidade em tudo.
Crucificar a carne
Os que são de Cristo crucificaram a carne com suas paixões e concupiscências. O domínio próprio é fruto do Espírito Santo.
Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa.
Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.
Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.
don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
Tudo para a glória de Deus
Quer comamos, quer bebamos, tudo deve ser feito para a glória de Deus. Devemos fugir das paixões que guerreiam contra a alma.
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.
Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.
Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.