Pular para o conteúdo
Publicidade

Palavras de conforto

Por Bíblia Online

Deus é o Deus de todo conforto. Ele consola os que choram, restaura os quebrantados e promete que a dor presente dará lugar à alegria eterna.

O Deus de toda consolação

Bendito seja o Deus e Pai de nosso Senhor Jesus Cristo, Pai das misericórdias e Deus de toda consolação, que nos consola em todas as tribulações.

Allah na dukan ta’aziyya

Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.

Allah na dukan ta’aziyya

Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.

Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.

Gama bai rena ko ƙyale

wahalar masu shan wuya ba;

bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba

amma ya saurari kukansa na neman taimako.

Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

Promessas de restauração

Deus sarará o quebrantado de coração e atará as suas feridas. Quem semeia em lágrimas, colherá com júbilo.

Ya warkar da masu raunanar zuciya

ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

amma alherinsa har matuƙa ne;

mai yiwuwa a yi kuka da dare

amma farin ciki kan zo da safe.

Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

kullum yana a shirye taimaka a lokacin wahala.

Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji

zai kuwa riƙe ku;

ba zai taɓa barin

mai adalci fāɗi ba.

Ka lissafta makokina;

ka jera hawayena a littafinka,

ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,

mafaka a lokutan wahala.

Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka.

Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

Paz e descanso

Jesus disse: 'Vinde a mim, todos os cansados e sobrecarregados, e eu vos aliviarei.' A paz de Deus que excede todo entendimento guarda o coração.

"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.

Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."

Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.

Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

Esperança eterna

Deus enxugará toda lágrima. A dor presente é momentânea, mas a glória futura é eterna. O Senhor transforma luto em dança.

Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, "Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe."

Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. "Ina yin kome sabo!" Sai ya ce, "Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma."

Bari Allah na bege cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

Shekarar tagomashin Ubangiji

Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

domin Ubangiji ya shafe ni

domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

don in yi shelar yanci don ɗaurarru

in kuma kunce yan kurkuku daga duhu

don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

in maido musu rawani mai kyau

a maimako na toka,

man murna

a maimako na makoki,

da kuma rigar yabo

a maimako na ruhun fid da zuciya.

Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

shukin Ubangiji

don bayyana darajarsa.

Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta

haka zan ta’azantar da ku;

za ku kuma ta’azantu a Urushalima."

Nunca sozinhos

Deus nunca nos abandona. Ele está ao nosso lado em cada vale, segura nossa mão e promete que o choro não durará para sempre.

Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

"Ba zan taɓa bar ka ba;

ba zan taɓa yashe ka ba."

Ubangiji nagari ne,

mafaka kuma a lokacin wahala.

Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,

Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

mai iko ne don ceto.

Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

zai rufe ki da ƙaunarsa,

zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa."

Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!

Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

Ko da na yi tafiya

ta kwari na inuwar mutuwa,

ba zan ji tsoron mugu ba,

gama kana tare da ni;

bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

za su yi mini ta’aziyya.

Abu guda na roƙi Ubangiji,

wannan shi ne na nema,

cewa in zauna a gidan Ubangiji

dukan kwanakin raina,

in dubi kyan Ubangiji

in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

Gama a lokacin wahala,

zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;

zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa

ya kuma sa ni can a bisa dutse.

Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce

alkawarinka yana kiyaye raina.

Yana ɗaukaka masu sauƙinkai,

yana kāre waɗanda suke makoki.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, sa’an nan kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da yan’uwa mata, da yan’uwa maza, da uwaye, da ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma sami rai madawwami.

Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.

Seja o primeiro