Pular para o conteúdo
Publicidade

Palavras de consolo

Por Bíblia Online

A Bíblia é repleta de palavras de consolo para os aflitos. Deus está perto dos que sofrem e promete enxugar toda lágrima, renovar a esperança e restaurar o coração partido.

Deus está conosco

O Senhor é refúgio e fortaleza. Mesmo no vale da sombra da morte, não precisamos temer — Ele está ao nosso lado para nos consolar.

Ko da na yi tafiya

ta kwari na inuwar mutuwa,

ba zan ji tsoron mugu ba,

gama kana tare da ni;

bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

za su yi mini ta’aziyya.

Ubangiji ne haskena da cetona,

wa zan ji tsoro?

Ubangiji ne mafakar raina,

wane ne zan ji tsoro?

Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,

mafaka a lokutan wahala.

Abu guda na roƙi Ubangiji,

wannan shi ne na nema,

cewa in zauna a gidan Ubangiji

dukan kwanakin raina,

in dubi kyan Ubangiji

in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

Gama a lokacin wahala,

zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;

zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa

ya kuma sa ni can a bisa dutse.

Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,

ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

Consolação e esperança

Deus consola os humildes e exalta os abatidos. Ele nunca nos desamparará.

Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."

Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku."

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Yana ɗaukaka masu sauƙinkai,

yana kāre waɗanda suke makoki.

Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,

Descanso e renovação

Bem-aventurados os que choram, pois serão consolados. A Bíblia nos convida a descansar nos braços do Pai e encontrar paz para a alma.

Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

Ka ba ni alamar alherinka,

don abokan gābana su gani su kuma sha kunya,

gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.

Bari ƙaunarka marar ƙarewa yi mini ta’aziyya,

bisa ga alkawarinka ga bawanka.

sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

Lokaci domin kowane abu

Akwai lokaci domin kowane abu,

da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.

Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa,

lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.

Lokacin kisa da lokacin warkarwa,

lokacin rushewa da lokacin ginawa.

Lokacin kuka da lokacin dariya,

lokacin makoki da lokacin rawa.

Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su,

lokacin runguma da lokacin dainawa.

Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya,

lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.

Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa,

lokacin yin shiru da lokacin magana.

Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya,

lokacin yaƙi da lokacin salama.

Seja o primeiro