Pular para o conteúdo
Publicidade

O pão da vida

Por Bíblia Online

Jesus se declarou o Pão da Vida — o alimento espiritual que satisfaz a fome mais profunda da alma humana. Quem come deste pão viverá para sempre.

Eu sou o Pão da Vida

Jesus disse: 'Eu sou o pão da vida; quem vem a mim nunca terá fome.' Ele é o sustento que sacia a alma eternamente.

Sa’an nan Yesu ya furta cewa, "Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.

Ni ne burodin rai.

Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, "Ni ne burodin da ya sauka daga sama."

Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa."

O pão que dá vida ao mundo

Jesus é o pão vivo que desceu do céu. Quem come da sua carne e bebe do seu sangue tem a vida eterna e será ressuscitado no último dia.

Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai."

Sai Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.

Yesu ya amsa ya ce, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.

Saciar a fome da alma

Bem-aventurados os que têm fome e sede de justiça, porque serão fartos. Nem só de pão vive o homem, mas de toda palavra que sai da boca de Deus.

Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,

gama za a ƙosar da su.

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake cewa, Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah."

Kada ku damu

"Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?

Seja o primeiro