Pular para o conteúdo
Publicidade

Pão

Por Bíblia Online

O pão é símbolo central na Bíblia: do maná no deserto ao pão da vida — Jesus. A Escritura usa o pão para ensinar sobre provisão divina, comunhão e dependência espiritual.

O maná do céu

Deus alimentou Israel no deserto com pão do céu. O maná era diário, fiel e suficiente — retrato da provisão constante de Deus.

Ubangiji ya ce wa Musa, "Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ "

Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani. Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, "Mene ne wannan?" Gama ba su san ko mene ne ba.

Musa ya ce musu, "Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.

Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma.

Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa

ya kuma buɗe ƙofofin sammai;

ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci,

ya ba su hatsin sama.

Mutane suka ci burodin mala’iku;

ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.

Yana sa ciyawa yi girma saboda shanu,

tsire-tsire domin mutum ya nome,

suna fid da abinci daga ƙasa,

ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum yi murna,

mai kuwa yakan sa fuska yi haske,

abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

O pão da vida

Jesus declarou: 'Eu sou o pão da vida.' Quem vem a Ele nunca terá fome, e quem nele crê jamais terá sede. Ele é o sustento eterno.

Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai."

Sai suka ce, "Ranka daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi."

Sa’an nan Yesu ya furta cewa, "Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.

Ni ne burodin rai. Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai."

Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake cewa, Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah."

Partilha e comunhão

O partir do pão une o corpo de Cristo. Na Ceia, na generosidade e na partilha, expressamos a comunhão com Deus e uns com os outros.

Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, "Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni."

Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har dawo.

Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.

"To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

" Ubanmu wanda yake cikin sama,

a tsarkake sunanka,

mulkinka zo

a aikata nufinka a duniya

kamar yadda ake yi a sama.

Ka ba mu yau abincin yininmu.

Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka,

gama yakan raba abincinsa da matalauta.

Sai ya amsa ya ce, "Ku, ku ba su wani abu su ci."

Suka ce masa, "Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?"

Sai ya yi tambaya ya ce, "Burodi nawa kuke da su? Je ku duba."

Da suka duba, sai suka ce, "Biyar da kifi biyu."

Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.

Provisão divina

O justo não é desamparado e seus descendentes não mendigam pão. Deus provê com fidelidade o alimento de cada dia.

ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

ko a ce ya’yansu suna roƙon burodi.

Yistin Farisiyawa da Sadukiyawa

Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. Yesu ya ce musu, "Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa."

Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, "Ko don ba mu kawo burodi ba ne."

Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, "Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa." Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Burodi a bisa ruwaye

Ka jefa burodinka a bisa ruwaye,

gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.

Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas,

gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.

Seja o primeiro