Pular para o conteúdo
Publicidade

Perseguição

Por Bíblia Online

Jesus advertiu que seus seguidores seriam perseguidos pelo mundo. Mas a perseguição não é sinal de fracasso — é sinal de fidelidade. Bem-aventurados os que sofrem por causa da justiça.

Perseguição como marca do discípulo

Jesus disse: se o mundo vos odeia, sabei que antes de vós odiou a mim. Todo o que quer viver piedosamente será perseguido.

Duniya ta ƙi jinin almajirai

"In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.

Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.

Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,

gama mulkin sama nasu ne.

"Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.

Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,

suka ware ku, suka zage ku,

suna ce da ku mugaye,

saboda Ɗan Mutum.

Recompensa na perseguição

Os perseguidos por causa de Cristo receberão grande galardão no céu. Quem perde por amor ao evangelho receberá cem vezes mais.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, sa’an nan kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da yan’uwa mata, da yan’uwa maza, da uwaye, da ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma sami rai madawwami.

Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?

Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

Amor e confiança em meio à adversidade

A Bíblia nos ensina a amar nossos perseguidores, abençoar os que nos maldizem e confiar que nossos tempos estão nas mãos de Deus.

Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,

Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.

Lokutana suna a hannuwanka;

ka cece ni daga abokan gābana

da kuma daga waɗanda suke fafara ta.

Ko da na yi tafiya

ta kwari na inuwar mutuwa,

ba zan ji tsoron mugu ba,

gama kana tare da ni;

bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

za su yi mini ta’aziyya.

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?

Seja o primeiro