Publicidade

Gravidez e maternidade

Por Bíblia Online

Gravidez e maternidade são bênçãos celebradas na Bíblia. Deus forma cada criança no ventre, cuida da mãe e da família, e abençoa a geração dos justos.

Filhos são herança do Senhor

Deus abençoa a fertilidade e o crescimento das famílias. Cada criança é obra de suas mãos, conhecida e amada antes mesmo de nascer.

Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za kasance babu haihuwa.

amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su.

Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;

tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

sa’ad da aka yi ni asirce.

Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

Idanunka sun ga jikina marar fasali;

dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

kafin ɗayansu kasance.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Zan kai mace har haihuwa

in kuma sa ta kāsa haihu?" In ji Ubangiji.

"Zan rufe mahaihuwa

sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?" In ji Allahnku.

Força e cuidado na gravidez

Deus dá forças à mulher grávida e a sustenta em cada etapa. Sua graça é suficiente e seu poder se aperfeiçoa na fraqueza.

Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

Amma ya ce mini, "Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona." Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi zauna tare da ni.

Ka juye kunnenka gare ni,

ka zo da sauri ka cece ni;

ka zama dutsen mafakata,

mafaka mai ƙarfi na cetona.

Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,

na yi kira yayinda zuciyata ta karai;

ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

Yakan lura da garkensa kamar makiyayi.

Yakan tattara tumaki wuri ɗaya

riƙe su kurkusa da ƙirjinsa;

a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.

"Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,

dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,

ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,

na kuma riƙe ku tun haihuwarku.

Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

Na yi ku zan kuma riƙe ku;

zan lura da ku

in kuma kuɓutar da ku.

A bênção da maternidade

A Bíblia honra a maternidade como ministério sagrado. As mães são instrumentos de Deus para formar vidas e transmitir a fé.

Amma mata Za sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.

Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;

haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,

Kayinu da Habila

Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, "Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji."

Haihuwar Ishaku

Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.

Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.

Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, "Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji."

Proteção divina

Deus protege a mãe e o bebê, guardando-os de todo mal. Ele acompanha cada momento com ternura e fidelidade.

Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

Zan ce game da Ubangiji, "Shi ne mafakata da kagarata,

Allahna, wanda nake dogara."

Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

zai tsare ranka;

Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

yanzu da har abada kuma.

"Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,

kafin a haife ka, na keɓe ka;

na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai."

"Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai,

"Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

Mai yiwuwa ta manta,

amma ba zan taɓa manta da ke ba!

Esperança e promessa

A maternidade é caminho de esperança. Como Sara, Ana e Isabel, as mães encontram na fé a força para aguardar as promessas de Deus.

Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.

Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!"

Waƙar Maryamu

Sai Maryamu ta ce,

"Raina yana ɗaukaka Ubangiji

ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.

Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,

sunansa labudda Mai Tsarki ne.

Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta

ta zama kamar mahaifiyar ya’ya mai farin ciki.

Yabi Ubangiji.

Zan sa mata albarka, ban da haka ma, zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za kuwa zama mahaifiyar al’ummai; sarakunan mutane za su fito daga gare ta."

Matarka za zama kamar kuringar inabi mai ya’ya

a cikin gidanka;

ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

kewaye da teburinka.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-