Pular para o conteúdo
Publicidade

Raiva

Por Bíblia Online

A raiva é uma emoção humana que a Bíblia trata com seriedade. Irar-se não é pecado em si, mas a ira descontrolada destrói relacionamentos e abre porta para o mal.

Controlar a ira

A Bíblia nos exorta a ser tardios para irar-se. A resposta branda desvia o furor, e o que se controla é mais forte que um guerreiro.

Saurarawa da kuma aikatawa

Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi,

amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa,

amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.

Wawa yakan nuna fushinsa a fili,

amma mai hikima kan kanne fushinsa.

Wawa kan nuna fushinsa nan take,

amma mai la’akari kan ƙyale zargi.

Irar-se sem pecar

Paulo ensina: irai-vos, mas não pequeis. Não deixe o sol se pôr sobre a vossa ira, para não dar lugar ao diabo.

"Cikin fushinku kada ku yi zunubi." Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama.

Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,

amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

Girmankai kan jawo faɗa ne kawai,

amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.

Amor e perdão acima da raiva

O amor cobre multidão de pecados. A Bíblia nos chama a não alimentar rancor, mas a perdoar e amar, vencendo a raiva com compaixão.

Ƙiyayya kan haddasa wahala,

amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

" Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

" Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.

Ya ci gaba, "Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum."

Ku lura fa, yan’uwa, cewa kada waninku kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.

"In mutum ya saki matarsa

ta kuwa bar shi ta auri wani mutum,

zai iya komo da ita kuma?

Ƙasar ba za ƙazantu gaba ɗaya ba?

Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa

yanzu za ki komo wurina?"

In ji Ubangiji.

"Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.

Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba?

A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki,

kin zauna kamar makiyayi a hamada.

Kin ƙazantar da ƙasar

da karuwancinki da muguntarki.

Saboda haka an hana yayyafi,

kuma babu ruwan bazara da ya sauka.

Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;

kin ƙi ki ji kunya.

Yanzu ba kin kira ni,

Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,

kullum za ka riƙa fushi?

Hasalarka za ci gaba har abada ne?

Haka kike magana,

amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi."

Isra’ila marar aminci

A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, "Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za komo wurina amma ba yi haka ba, yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. Duk da wannan duka, Yahuda yar’uwarta rashin amincin ba komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce," in ji Ubangiji.

Ubangiji ya ce mini, "Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,

" Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,in ji Ubangiji,

Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

gama ni mai jinƙai ne,in ji Ubangiji,

Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

Ki dai yarda da laifinki

kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye,

kin watsar da alheranki ga baƙin alloli

a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa,

ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ "

in ji Ubangiji.

"Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya," in ji Ubangiji, "gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar," in ji Ubangiji, "mutane ba za su ƙara yin magana a kan, Akwatin alkawarin Ubangiji ba.Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.

"Ni kaina na faɗa,

" Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ya’yana maza

in ba ki ƙasa mai daɗi,

gādo mafi kyau da wata al’umma.

Na zaci za ki kira ni Mahaifi

ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.

Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,

haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,"

in ji Ubangiji.

An ji kuka a filayen tuddai,

kuka da roƙon mutanen Isra’ila,

domin sun lalace hanyoyinsu

sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.

"Ku komo, mutane marasa bangaskiya;

zan warkar da ku daga ja da bayanku."

"I, za mu zo wurinka,

gama kai ne Ubangiji Allahnmu.

Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai

da duwatsu banza ne;

tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne

akwai ceton Isra’ila.

Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu

amfanin wahalar kakanninmu

garkunan tumakinsu da na awakinsu,

yaransu maza da mata.

Bari mu kwanta mu sha kunya,

bari kuma kunyarmu ta rufe mu.

Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi,

da mu da kakanninmu;

daga ƙuruciyarmu har zuwa yau

ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba."

Luciano Januzelli
1 pessoa deu Amém