Reconhecer
Reconhecer a Jesus como Senhor é o fundamento da fé cristã. A confissão de fé é o ato de declarar publicamente quem Jesus é e a quem pertencemos.
Confissão e salvação
Se confessarmos com a boca que Jesus é Senhor e crermos no coração que Deus o ressuscitou, seremos salvos.
Cewa in ka furta da bakinka, "Yesu Ubangiji ne," ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.
Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
A rubuce yake cewa,
" ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji,
‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana;
kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ "
kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,
don ɗaukakar Allah Uba.
Reconhecer a fé
Reconhecer a Jesus é um ato de coragem e compromisso. Quem o confessar diante dos homens, Ele confessará diante do Pai.
Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.
Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
Reconhecer o pecado e a bondade de Deus
Reconhecer nossos pecados é o caminho para o perdão. E reconhecer que o Senhor é nossa porção nos dá esperança inabalável.
Sa’an nan na furta zunubina a gare ka
ban kuwa ɓoye laifina ba.
Na ce, "Zan furta
laifofina ga Ubangiji."
Ka kuwa gafarta
laifin zunubina. Sela
Na ce wa kaina, "Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi."
Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka?
Ubangiji Maɗaukaki,
shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela