Repouso e férias
Deus criou o descanso como parte da vida. O sábado, o repouso e até as férias refletem a confiança de que Deus sustenta todas as coisas — mesmo quando paramos.
O descanso como ordenança
Deus descansou no sétimo dia e nos convidou a fazer o mesmo. O descanso sabático é um presente de Deus para restauração do corpo e da alma.
Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa.
"In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci
da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki,
in kuka kira Asabbaci ranar murna
rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma,
in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama
da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu,
sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji,
zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe
ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub."
Ni Ubangiji ne na faɗa.
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Sono e paz
Ditar-se em paz e dormir tranquilamente é bênção do Senhor. Quem confia nele dorme sem medo e acorda renovado.
Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
Na kwanta na yi barci;
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
Banza ne ka farka da wuri
ka koma da latti,
kana fama don abincin da za ka ci,
gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;
sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,
ko yă ci kaɗan ko da yawa,
amma yalwar mai arziki
ba ta barinsa yă iya yin barci.
Descanso e segurança
No repouso, encontramos segurança. Deus guarda os justos, e mesmo no silêncio da noite, sua paz nos protege e restaura.
Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro,
da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
Waɗanda suke aikata abin da yake daidai
sukan shiga da salama;
sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.