Descansar no Senhor
Descansar no Senhor é um ato de fé. Em um mundo agitado, Deus nos convida a entregar nossas ansiedades, aquietar o coração e confiar plenamente em sua provisão e cuidado.
O convite ao descanso
Jesus convida os cansados e sobrecarregados a irem a Ele e encontrar descanso para as suas almas. O jugo dele é leve.
"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne."
Ka natsu a gaban Ubangiji
ka kuma jira da haƙuri gare shi;
kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,
sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
"Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;
za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,
za a ɗaukaka ni cikin duniya."
Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,
gama Allah ne mafakarmu. Sela
Confiança e paz
Quem confia no Senhor encontra paz perfeita. A ansiedade perde o poder quando entregamos tudo nas mãos do Deus soberano.
Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,
"Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake,
cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku,
amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.
Aikin adalci zai zama salama;
tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
Esperar no Senhor
Esperar no Senhor renova as forças. A Bíblia nos ensina que aquietar-se diante de Deus e confiar em seu tempo é marca da maturidade espiritual.
Ka dogara ga Ubangiji,
ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya
ka kuma dogara ga Ubangiji.
Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
Cikin fushinku kada ku yi zunubi;
sa’ad da kuke kan gadajenku,
ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela
Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
A fidelidade de Deus
Deus é fiel. Seus planos são de paz e esperança. Podemos descansar sabendo que Ele guarda e sustenta quem nele confia.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
"Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.
Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;
ganyayensa kullum kore suke.
Ba shi da damuwa a shekarar fări
ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya."
Ubangiji ya amsa ya ce, "Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya."
Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.
Ya ce wa Yahuda, "Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe." Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.
Suna dab da ƙarshen gari, sai Sama’ila ya ce wa Shawulu, "Ka ce wa bawanka yă yi gaba, kai ka ɗan dakata a nan tukuna, domin in ba ka saƙo daga Allah."