O sangue de Jesus
O sangue de Jesus é o fundamento da redenção cristã. Através do seu sangue derramado na cruz, recebemos perdão, purificação e acesso à presença de Deus.
O poder redentor do sangue
O sangue de Cristo é o preço do nosso resgate. Sem derramamento de sangue não há remissão de pecados, e Cristo ofereceu o sacrifício perfeito e definitivo.
Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.
Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa.
Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.
Perdão e purificação
O sangue de Jesus nos purifica de todo pecado. Nele temos redenção e perdão, segundo as riquezas de sua graça.
Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah
Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya.
Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa,
Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba
Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa!
O sangue da aliança
Desde o Êxodo, o sangue é sinal de aliança entre Deus e seu povo. O sangue do Cordeiro pascal prefigurava o sacrifício supremo de Cristo.
Sa’an nan Musa ya kira dukan dattawan Isra’ila ya ce musu, "Ku je da sauri ku zaɓi dabbobin iyalanku, ku yanka ragon Bikin Ƙetarewa. Ku ɗauki ƙunshin itacen hizzob, ku tsoma cikin jinin da yake a kwano, ku yayyafa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada wani daga cikinku yă fita daga ƙofar gidansa sai da safe. Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.
Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.
"Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
"Duk wanda ya zub da jinin mutum,
ta hannun mutum za a zub da jininsa;
gama a cikin siffar Allah ne,
Allah ya yi mutum.
" ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.
Vitória pelo sangue
Os cristãos vencem o acusador pelo sangue do Cordeiro e pela palavra do seu testemunho. O sangue comprou para Deus gente de toda tribo e língua.
Sun ci nasara a kansa
ta wurin jinin Ɗan Ragon
da ta wurin kalmar shaidarsu;
ba su ƙaunaci rayukansu sosai
har da za su ja da baya daga mutuwa.
Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.
Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
Sai Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.