Pular para o conteúdo
Publicidade

Santa ceia

Por Bíblia Online

A Santa Ceia é uma das ordenanças mais sagradas da igreja cristã. Instituída por Jesus na última noite antes da crucificação, ela celebra seu sacrifício e proclama sua morte até que Ele volte.

A instituição por Jesus

Na noite em que foi traído, Jesus tomou o pão e o cálice, deu graças e os compartilhou com os discípulos, dizendo: 'Fazei isto em memória de mim.'

Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, "Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne."

Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, "Ku shassha daga cikinsa, dukanku. Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, "Ku karɓa, wannan jikina ne."

Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

Sai ya ce musu, "Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. Gaskiya nake gaya muku, Ba zan ƙara sha daga ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ "

Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, "Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni."

Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, "Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.

O significado espiritual

A Ceia é participação no corpo e no sangue de Cristo. Jesus ensinou que quem come de sua carne e bebe de seu sangue tem a vida eterna.

Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai."

Sai Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa. Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada."

bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, "Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni." Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, "Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni." Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har dawo.

Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. Dole kowa bincike kansa kafin ci burodin kuma sha daga kwaf ɗin.

Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har dawo.

A prática da Igreja

Desde os primeiros cristãos, a Ceia do Senhor é parte fundamental da vida comunitária da Igreja, celebrada com reverência e exame de consciência.

Zumuncin masu bi

Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.

Ta da Yutikus daga matattu a Toruwas

A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.

Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.

Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. Dole kowa bincike kansa kafin ci burodin kuma sha daga kwaf ɗin. Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne.

Seja o primeiro