Saúde
A saúde é uma bênção de Deus. A Bíblia ensina que Deus é nosso curador, que devemos cuidar do corpo como templo do Espírito e que a alegria do Senhor renova nossas forças.
Deus, o nosso curador
O Senhor é quem sara todas as nossas doenças. Ele prometeu abençoar o pão e a água e tirar as enfermidades do meio do seu povo.
Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.
Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
Da jin wannan, Yesu ya ce, "Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
O corpo como templo
Nosso corpo é templo do Espírito Santo. A Bíblia nos encoraja a cuidar da saúde física com disciplina e reverência a Deus.
Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.
Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.
Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
A alegria que cura
O coração alegre é bom remédio. A esperança do coração traz alegria, e as palavras agradáveis são como favo de mel — doçura para a alma e saúde para o corpo.
Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma,
mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka
ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,
gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.