Publicidade

Sonhos

Por Bíblia Online

Sonhos aparecem em toda a Bíblia como meio de revelação divina. Deus falou através de sonhos a patriarcas, profetas e servos, mas também alertou contra falsos sonhadores.

Sonhos como revelação divina

Deus usou sonhos para comunicar sua vontade a homens e mulheres ao longo da história bíblica, revelando caminhos e mistérios.

sai ya ce, "Ku ji abin da zan faɗa,

"Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku,

nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi,

in yi magana da shi cikin mafarkai.

Ranar Ubangiji

"Daga baya kuma,

zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.

Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

tsofaffinku za su yi mafarkai,

matasanku za su ga wahayoyi.

Bitrus ya yi wa taron jawabi

Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, "Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

"Allah ya ce, A kwanakin ƙarshe,

zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.

Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

samarinku za su ga wahayoyi,

dattawanku kuma za su yi mafarkai.

Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

Sarki ya tambayi Daniyel (wanda ake kira Belteshazar), za ka iya faɗa mini mafarkin da na yi ka kuma fassara shi?

Daniyel ya amsa, "Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,

Sonhos na história da Bíblia

De José no Egito a José pai de Jesus, Deus guiou a história da salvação através de sonhos, protegendo e dirigindo seu povo.

Sai suka amsa, "Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su."

Sa’an nan Yusuf ya ce musu, "Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku."

Fir’auna ya ce wa Yusuf, "Na yi mafarki, kuma babu wanda ya iya fassara shi. Amma na ji an ce sa’ad da ka ji mafarki, kana iya fassara shi."

Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, "Ba ni ne da iyawar ba, Allah zai iya ba wa Fir’auna amsar da yake nema."

Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. Za haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu."

Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, "Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi."

Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,

mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

Sabedoria sobre sonhos

A Bíblia ensina discernimento: nem todo sonho vem de Deus. Devemos entregar nossos planos ao Senhor e confiar na direção dele.

Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,

shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.

Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,

amma manufar Ubangiji ce takan cika.

Bautar waɗansu alloli

In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, "Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada," kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

"Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, Na yi mafarki! Na yi mafarki!Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?

Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya," in ji Ubangiji. "Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan," in ji Ubangiji.

Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa,

haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.

Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-