Publicidade

Superação

Por Bíblia Online

Superar desafios, dificuldades e tentações faz parte da caminhada cristã. A Bíblia nos garante que, em Cristo, somos mais que vencedores em todas as circunstâncias.

Vitória em Cristo

Jesus já venceu o mundo. Nele temos coragem, paz e a certeza de que nenhuma adversidade poderá nos derrotar definitivamente.

"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."

"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."

A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.

Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.

Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

Sun ci nasara a kansa

ta wurin jinin Ɗan Ragon

da ta wurin kalmar shaidarsu;

ba su ƙaunaci rayukansu sosai

har da za su ja da baya daga mutuwa.

Superando o mal com o bem

O cristão vence o mal não com violência, mas com o bem. O amor, a fé e a perseverança são as armas da superação.

Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.

Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.

In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, don kada Shaiɗan rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.

Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.

Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.

Força e coragem divina

Deus é nosso escudo e fortaleza. Quando o medo tenta nos paralisar, a presença do Senhor nos fortalece e nos encoraja a prosseguir.

Ta Dawuda.

Ubangiji ne haskena da cetona,

wa zan ji tsoro?

Ubangiji ne mafakar raina,

wane ne zan ji tsoro?

Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

Ba na dogara ga bakana,

takobina ba ya kawo nasara;

amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,

ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.

A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini,

kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela

Ya Ubangiji, ka cece mu;

Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.

Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji.

Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.

Duba, Ubangiji Allahnku ya ba ku ƙasar. Ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allahn kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro, kada ku fid da zuciya."

Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, ba ku nasara."

Za ka kiyaye shi da cikakken salama

shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

domin ya dogara a gare ka.

Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

Ku, ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

Ku, ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

Resistindo a tentação

A armadura de Deus nos protege contra as investidas do mal. Resistir ao diabo, vigiar e orar são essenciais para a superação espiritual.

Kayan yaƙi na Allah

A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji ba ku ƙarfi. Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya zama ɗamararku, adalci zama sulkenku, shirin kai bisharar salama zama kamar takalmi a ƙafafunku. Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta , wadda take lalacewa saboda sha’awace-shaawacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

"Cikin fushinku kada ku yi zunubi." Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama.

Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.

Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada ce, "Allah ne yake jarrabtarsa." Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.

Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.

Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-shaawace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.

Perseverança até o fim

A corrida da fé exige perseverança. Devemos lançar fora todo peso e olhar para Jesus, o autor e consumador da nossa fé.

Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.

Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.

Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram.

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?

Fiye da masu nasara

Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, kuma tsare ku daga mugun nan.

Descanso e renovação

Jesus convida os cansados e sobrecarregados a descansar nele. Sua graça é suficiente para nos renovar em meio às tribulações.

"Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

"Ba zan taɓa bar ka ba;

ba zan taɓa yashe ka ba."

Gama ba abin da zai gagari Allah."

Ya tambaye su, "Don me kuke barci? Ku tashi ku yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba."

Da ya kai wurin, sai ya ce musu, "Ku yi addu’a don kada ku fāɗi cikin jarraba."

Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.

Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne."

Zuwan sarkin Sihiyona

Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima!

Ki yi sowa, Diyar Urushalima!

Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki,

mai adalci yana kuma da ceto,

mai tawali’u yana kuma hawan jaki,

yana a kan ɗan aholaki, a kan yar jaka.

Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don rushe aikin Iblis.

Ina rubuta muku, ya’yana ƙaunatattu,

domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

Ina rubuta muku, ubanni,

domin kun san shi wanda yake tun farko.

Ina rubuta muku, samari,

domin kun ci nasara a kan mugun nan.

Ina rubuta muku, ya’yana ƙaunatattu,

domin kun san Uba.

Ina rubuta muku, ubanni,

domin kun san shi wanda yake tun farko.

Ina rubuta muku, samari,

domin kuna da ƙarfi,

maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,

kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

Kada ku ƙaunaci duniya

Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.

Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, "Biyun za su zama jiki ɗaya." Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

Rayuwa ta wurin Ruhu

Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-shaawacen mutuntaka ba. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.

Seja o primeiro
Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-28_14-13-17-