Pular para o conteúdo
Publicidade

Sobre ter filhos

Por Bíblia Online

Filhos são uma dádiva do Senhor, uma herança que Deus confia aos pais. A Bíblia celebra a maternidade e a paternidade como vocações sagradas e fontes de bênção.

Filhos: herança do Senhor

A Escritura declara que os filhos são bênção de Deus. Cada criança é um presente precioso confiado aos pais para ser cuidado com amor.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Matarka za zama kamar kuringar inabi mai ya’ya

a cikin gidanka;

ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

kewaye da teburinka.

Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta

ta zama kamar mahaifiyar ya’ya mai farin ciki.

Yabi Ubangiji.

Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."

Instruir nos caminhos de Deus

A Bíblia orienta os pais a instruir seus filhos nos caminhos do Senhor desde cedo, com dedicação, disciplina e exemplo.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku. Ku koyar da su ga ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;

zai ba ka farin cikin da kake so.

Cada vida é preciosa

Deus conhece e forma cada criança no ventre. Antes de nascer, Ele já nos separou e preparou um propósito para cada vida.

"Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,

kafin a haife ka, na keɓe ka;

na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai."

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

sa’ad da aka yi ni asirce.

Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

Daga leɓunan yara da jarirai

ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka

da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."

Seja o primeiro