Trabalho
O trabalho é uma ordenança divina desde a criação. Deus colocou o homem no jardim para cultivar e guardar, revelando que o labor é parte do propósito humano e um meio de glorificá-lo.
Trabalho como vocação divina
Deus nos criou para trabalhar com propósito. O trabalho é expressão da imagem divina em nós e deve ser feito como para o Senhor.
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Ku yi kome da ƙauna.
Diligência e recompensa
A mão diligente enriquece, mas a preguiça traz pobreza. A Bíblia valoriza o esforço honesto, dedicado e perseverante em toda obra.
Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,
amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,
amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba,
amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
Ba shi da jagora
ba shugaba ko mai mulki,
duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
Yaushe za ku farka daga barcinku?
Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
rashi kuma kamar ɗan fashi.
Wanda yake ragwanci a aikinsa
ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;
ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
Albarkar Ubangiji kan kawo wadata,
ba ya kuma ƙara wahala a kai.
Planejamento e excelência
A excelência no trabalho honra a Deus. Devemos nos dedicar com competência, entregar nossos planos ao Senhor e buscar o melhor em cada tarefa.
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi,
shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
Faɗi 6
Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa?
Zai yi wa sarakuna hidima;
ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya
O contentamento no trabalho
Deus nos dá a capacidade de desfrutar do nosso trabalho. Poder comer, beber e encontrar satisfação em nosso labor é um dom divino.
Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.
Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa.
Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah.
Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
Akwai wani mutum shi kaɗai;
bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.
Ba shi da hutu daga wahalarsa,
duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.
Ya tambayi kansa, "Ma wane ne nake wannan wahala,
kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?"
Wannan ma ba shi da amfani,
harkar baƙin cikin ne kawai!
Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
A responsabilidade cristã
O cristão deve trabalhar com suas próprias mãos, viver dignamente e ser exemplo de dedicação. Quem não trabalha, não coma.
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, "In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci."
Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa.
Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;
ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,
I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.
Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?
Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.
Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.