Tristeza
A tristeza faz parte da experiência humana, mas a Bíblia nos assegura que Deus está perto dos que sofrem. Ele enxuga as lágrimas e transforma a dor em esperança.
Deus consola os aflitos
O Senhor está perto dos quebrantados de coração. Mesmo no vale mais escuro, sua presença é refúgio e consolo para a alma que chora.
Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
Ubangiji yakan ba wa makafi ido,
Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,
Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji;
ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu ta’aziyya.
"Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji.
A alegria virá
A dor tem prazo de validade. A manhã de alegria sempre vem depois da noite de choro. Deus promete transformar o luto em dança.
Gama fushinsa na ɗan lokaci ne
amma alherinsa har matuƙa ne;
mai yiwuwa a yi kuka da dare
amma farin ciki kan zo da safe.
Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, "Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe."
‘Ba za su sāke jin yunwa ba;
ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.
Rana ba za tă buga su ba,’
ko kuma kowane irin zafin ƙuna.
Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;
‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’
‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ "
cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
Entregando a dor a Deus
Podemos lançar sobre o Senhor toda nossa ansiedade e tristeza, porque Ele cuida de nós com ternura e não nos abandona.
Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai."
Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
O choro e o arrependimento
Há tristezas que produzem arrependimento e conduzem à vida. O choro diante de Deus é acolhido e transformado em bênção.
"Ko yanzu", in ji Ubangiji,
"Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,
da azumi da kuka da makoki."
Kuringar inabin ta bushe
itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,
’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,
dukan itatuwan filaye, sun bushe.
Tabbatacce farin cikin ’yan adam
ya bushe.
Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada ya ce,
"Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,
tsirara kuma zan koma.
Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;
yabo ya tabbata ga Ubangiji."
Karin maganar Solomon.
Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.
Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka
ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,
gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.
Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.