Vaso
A metáfora do vaso é uma das mais belas da Bíblia. Assim como o oleiro molda o barro, Deus nos forma segundo seus propósitos, fazendo de nós vasos úteis para sua glória.
Nas mãos do oleiro
Deus é o Oleiro e nós somos o barro. Ele tem autoridade e sabedoria para nos moldar conforme sua vontade perfeita, e não devemos questionar sua obra.
Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu.
Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane;
dukanmu aikin hannunka ne.
A gidan mai ginin tukwane
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. "Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona." Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, "Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?" In ji Ubangiji. "Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.
Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? "Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ " Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
"Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,
da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.
Yumɓu ya iya ce wa magini,
‘Me kake yi?’
Aikinka na iya cewa,
‘Ba shi da hannuwa’?
Kuna birkitar abubuwa,
sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu!
Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi,
"Ba shi ne ya yi ni ba"?
Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane,
"Ba ka san kome ba"?
Vasos para honra
O cristão é chamado a ser um vaso de honra, purificado e preparado para toda boa obra. Nosso valor está em quem nos formou e no que carregamos.
A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.
Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.
Dubi samarin Sihiyona masu daraja,
waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya,
yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa,
aikin maginin tukwane!
Moldados pela graça
Mesmo quando nos sentimos frágeis e imperfeitos, o poder de Deus se aperfeiçoa em nossa fraqueza. Ele nos restaura e nos renova continuamente.
"Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni.
Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu.
Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba
haka leɓuna masu mugun zuciya.
Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya;
ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke.
Gama lokacin da za a yanka ku ya zo;
za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.