45 Haka yake a rubuce cewa, "Adamu, mutumin farko ya zama mai rai"15.45 Far 2.7; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. 46 Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. 47 Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. 48 Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. 49 Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.
Publicidade